Isa ga babban shafi
Najeriya-Tsaro

"Yan ta'adda sun kashe sojojin Najeriya biyu

Sojojin Najeria a Damboa, jihar Borno.
Sojojin Najeria a Damboa, jihar Borno. STEFAN HEUNIS/AFP

Sojojin Najeriya 2 ne suka mutu a wata arangama tsakanin dakarun kasar da mayakan kungiyar ‘yan ta’adda a jihar Adamawa dake arewa maso gabashin kasar.

Talla

Majiyoyi, kuma ganau sun ce a talatainin daren Juma’a ne ‘yan ta’adda makare a motocin akori kura suka shiga garin Garkida, kuma suka shiga kai wa dakaru najeriya farmaki ba kakkautawa, lamarin da ya tilasta al’umma garin tserewa zuwa tsaunuka don neman tsira.

Babu kungiyar dai da ta dau alhakin harin, sai dai ana ganin kungiyar mujahidai masu mubayi’a da IS ne suka kai harin.

Babu farar hular da aka jikkata a wannan harin sakamakon arcewa da suka yi zuwa tsaunuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.