Isa ga babban shafi
Afrika

Kamto ya bukaci taimakon kasashen duniya domin sasanta rikicin Kamaru

Maurice Kamto, jagoran 'yan adawan Kamaru
Maurice Kamto, jagoran 'yan adawan Kamaru REUTERS/Zohra Bensemra

Shugaban Yan adawar Kamaru Maurice Kamto ya ce kofa a bude take ga kasashen Duniyar dake neman sasanta rikicin kasar dake cigaba da lakume rayukan jama’a.

Talla

Yayin da yake jawabi ga magoya bayan sa a Douala, Kamto yace idan kawayen Kamaru na bukatar zuwa kasar domin taimaka musu shawo kan rikicin da ya addabe su, shi yana maraba da su.

Bayan kisan da aka yiwa fararen hula 23, shugaban Faransa Emmanuel Macron yayi alkawarin matsin lamba ga shugaba Paul Biya wajen shawo kan matsalar, kalaman da gwamnatin Kamaru da magoya bayan ta basu ji dadi a kai ba.

Fadar shugaban Kamaru tace Yan Kasar ne kawai zasu bukaci bayani daga shugaba Paul Biya amma ba shugaban wata kasa ba.

Jam’iyyar MRC ta Maurice Kamto ta umurci magoya bayan ta da su kauracewa zaben Yan majalisun da akayi saboda rikicin dake gudana tsakanin soji da Yan aware, wanda yayi sanadiyar mutuwar akalla mutane 300,000, yayin da sama da 700,000 suka tsere daga muhallin su a yankunan da ake amfani da Turancin Ingilishi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.