Isa ga babban shafi
Somalia

Sama da kasashe 100 sun sha alwashin tallafawa Somalia

Wasu mata 'yan gudun hijira a Arewacin kasar Somalia.
Wasu mata 'yan gudun hijira a Arewacin kasar Somalia. REUTERS/Baz Ratner/File Photo

Asusun bada lamuni na duniya IMF yace kasashe sama da 100 sun yi alkawarin bada agajin dala miliyan 334 domin biyawa Somalia basukan da ake bin ta, abinda zai bude baiwa kasar kofar samun kudade.

Talla

Shugabar hukumar Kristalina Georgieva wadda ta bayyana wannan matakin, tace agajin da wadannan kasashe suka bayar, zai taimakawa Somalia gaya, ganin irin dimbin matsalolin da suka addabe ta.

Wata kididdiga da aka fitar a karshen shekarar 2018, ta nuna cewar ana bin Somalia bashin da ya kai sama da dala biliyan 5, yayinda kasar ke bukatar kudade domin taimakawa jama’ar ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.