Isa ga babban shafi

Paul Biya ya samu rinjaye a zaben Kamaru

Wani sanye da rigar jam'iyyar mai mulkin kasar Kamaru RDPC kusa da motar soja
Wani sanye da rigar jam'iyyar mai mulkin kasar Kamaru RDPC kusa da motar soja AFP

Jam'iyyar Shugaba Paul Biya na Kamaru ta samu gagarumar nasara a zaben 'Yan Majalisun da aka yi ranar 9 ga wannan watan Fabarairu.

Talla

Shugaban Majalisar kula da tsarin mulkin kasar Clement Atangana ya sanar da cewar Jam’iyyar RDPC dake mulki ta samu kujeru 139 daga cikin kujeru 167 da aka bayyana.

Tuni aka soke zaben da akayi a mazabu 13 na Yankin da ake amfani da Turancin Ingilishi sakamakon matsalolin da aka samu, yayin da Majalisar tace za’a sake zabe a wadannan mazabu nan gaba.

A majalisar da aka zaba a shekarar 2013, Jam’iyyar RDPC ta Paul Biya ta samu kujeru 148, sai kuma Jam’iyyar SDF ta zo ta biyu da kujeru 18.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.