Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Wasu yan bindiga sun kashe jami'an tsaro a Burkina

Daya daga cikin kauyukan Burkina Faso
Daya daga cikin kauyukan Burkina Faso RFI/Pierre Pinto

A Burkina Faso akalla jami’an tsaro hade da sojin kasar 9 ne suka rasa rayukan su a yau asabar biyo bayan tagwayen harin da wasu yan bindinga dauke da muggan makamai suka kai zuwa bariqin yan Sanda na Sebba da kuma ayarin sojan kasar a arewacin Burkina Faso.

Talla

Maharan sunyi awon gaba da tarin makamai tareda raunata yan Sanda da dama, kasar ta Burkina Faso tsawon shekaru biyar kenan da take fama da matsalloli da suka jibanci tsaro a arewacin kasar, lamarin da ya tilastawa dubban mazauna arewacin kasar barin matsuginin su.

A farkon wannan watan majiyar tsaron kasar tace maharan haye kan babura sun afkawa kauyen na Bani ne dauke da muggan makamai, inda suka rika yiwa wadanda suka rutsa kisan gilla.

Wata majiyar tsaron ta ce kafin farmakin na ranar, sai da ‘yan ta’addar suka gargadi mazauna kauyen da su fice.

Harin na baya bayan nan ya zo ne bayan makamancinsa da aka kai kan kauyen Silgadji a lardin Soum ranar 25 ga Janairun da ya gabata, inda ‘yan ta’addar suka kashe mutane 39.

Wata kididdigar majalisar dinkin duniya ta ce rayukan akalla mutane dubu 4 suka salwanta a hare-haren ta’addanci cikin shekarar 2019 kadai, a kasashen Burkina Faso, Mali da kuma Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.