Isa ga babban shafi
Coronavirus

'Yan Afrika dubu 8 sun kamu da coronavirus

Afrika ta Kudu ce ke kan gaba wajen fama da coronavirus a nahiyar Afrika
Afrika ta Kudu ce ke kan gaba wajen fama da coronavirus a nahiyar Afrika RIJASOLO / AFP

Rahotanni daga Afrika na nuna cewar akalla mutane kusan 8,000 aka tabbatar suna dauke da cutar COVID-19 wadda ta shiga kasashe 50, yayin da ta kashe 332.

Talla

Alkaluman da aka bayar sun ce, kasashe 4 ne kacal ba a samu masu dauke da cutar ba, da suka hada da Comoros da Lesotho da Sao Tome and Principe sai kuma Sudan ta Kudu.

Cikin kasashen da cutar ta fi yawa sun hada da Afirka ta Kudu mai mutane 1,505, sai Algeria mai mutane 1,171, sai Masar mai mutane 985, sai Kamaru mai mutane 509.

Sauran sun hada da Tunis mai mutane 495, sai Burkina Faso mai mutane 302, sai Cote d’Ivoire mai mutane 218, sai Najeriya mai 210, kana Senegal mai 207.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.