Isa ga babban shafi
Benin

Kotu ta daure tsohon minista shekaru 20 a Jamhuriyar Benin

Shugaban Jamhuriyar Benin, Patrice Talon
Shugaban Jamhuriyar Benin, Patrice Talon RFI/FRance24

Kotu a jamhuriyar Benin ta yanke hukuncin daurin shekaru 20 a kan wani tsohon minista mai suna Komi Koutché da ke gudun hijira a Amurka, bayan samun sa da laifin handame makudaden kudaden kasar.

Talla

Komi Koutché, wanda ya rike mukamin ministan a lokacin mulkin tsohon shugaba Bony Yayi, ko baya ga hukuncin dauri, hakazalika kotu ta ci shit arar cfa milyan 500.

To sai dai kafin yanke hukuncin, lauyan tsohon ministan ya roki afuwa daga kotun, lura da cewa wanda yake karewa bai samu hallatar a gaban kotun ba, bisa dalilan cewa ya gaza fita daga Amurka saboda matakan da kasashe ke dauka biyo bayan bullar cutar Covid-19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.