Isa ga babban shafi
Coronavirus

WHO ta damu kan yaduwar coronavirus a Afrika

Hukumar Lafiya ta Duniya ta kadu da yaduwar coronavirus cikin sauri a nahiyar Afrika
Hukumar Lafiya ta Duniya ta kadu da yaduwar coronavirus cikin sauri a nahiyar Afrika premiumtimesng

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta bayyana damuwa kan ci gaba da karuwar yawan masu kamuwa da cutar coronavirus a Afrika, inda a yanzu adadin ya zarta dubu 10, yayin da kuma annobar ta halaka sama da mutane 500.

Talla

Rahoton hukumar ta WHO ya ce, yanzu haka sama da mutane dubu 10 da 420 ne suka kamu da cutar a Afrika, sannan kimanin 517 sun mutu.

Kasar Afrika ta Kudu na da mutane dubu 1 da 800 da suka harbu da cutar, amma 18 sun mutu, 45 kuma sun warke, sai Algeria inda annobar ta harbi sama da mutane dubu 1 da 460, ta kuma kashe wasu 200.

A Masar, kasar da annobar ta soma bulla ranar 14 ga Fabarairu a Afrika, sama da mutane dubu 1 da 320 suka kamu, wasu 85 sun mutu, sai Morocco mai mutane sama da dubu 1 da 150, wasu 83 sun rasu.

Hukumar Lafiyar ta Duniya ta ce, yanzu annobar ta coronavirus ko kuma COVID-19, ta kutsa kasashen nahiyar Afrika 52, ciki har da Najeriya da Ghana da Habasha da kuma Tunisia, inda a yanzu haka gwamnatocin kasashen suka dukufa wajen samar da karin dakunan gwaje-gwaje don gaggauta gano wadanda suka kamu da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.