Isa ga babban shafi
Najeriya-Coronavirus

Coronavirus ta kashe babban hadimin shugaban Najeriya Abba Kyari

Nigeria: Chief of Staff to President Muhammadu Buhari, Abba Kyari.
Nigeria: Chief of Staff to President Muhammadu Buhari, Abba Kyari. Sahara Reporters

Babban hadimin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wato Abba Kyari ya rasu a jiya juma’a sakamakon kamuwa da cutar Covid-19 wadda ya harbu da ita a karshen watan maris da ya gabata bayan dawowa daga wata ziyarar aiki da ya kai a kasar Jamus.

Talla

Fadar shugaban kasar ta tabbatar da rasuwar Abba Kyari a wata sanarwa da ta fitar cikin daren jiya. Bayan an tabbatar da cewa ya kamu da wannan cuta ta coronavirus a birnin Abuja, daga bisani an dauki Kyari zuwa Lagos domin jinya.

Abba Kyari dai ya kasance jami’in gwamnati mafi girma da cutar ta kashe a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.