Isa ga babban shafi
Nijar-Coronavirus

Mutane 639 ne suka harbu da Coronavirus a Nijar

Ministan lafiyar Nijar Dakta Iliasouu Idi Mainassara
Ministan lafiyar Nijar Dakta Iliasouu Idi Mainassara onep

An samu karin mutane 12 da suka harbu da cutar coronavirus cikin sa’o’i 24 da suka gabata a Jamhuriyar Nijar, inda adadin wadanda aka samu da cutar ya tashi zuwa 639, yayin da aka samu karin mutum daya da ya rasu, ma’ana dai adadin mamata ya tashi zuwa 19 a kasar.

Talla

A cikin sabbin mutanen da suka kamu da cutar a baya-bayan nan, 2 a jihar Zinder ne, 2 a Tillaberi, 1 a Dosso yayin da sauran 7 kuwa a birnin Yamai.

To sai dai ma’aikatar lafiyar jamhuriyar Nijar ta ce daga lokacin da wannan cuta ta bulla zuwa ranar asabar da ta gabata, mutane 113 ne suka warke daga cutar kuma tuni aka sallame su daga asibiti.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.