Isa ga babban shafi
Kamaru-Coronavirus

'Yan majalisar kasar Kamaru sun tara kudi don yaki da Covid-19

Jami'in lafiya rike da kwalbar maganin covid-19
Jami'in lafiya rike da kwalbar maganin covid-19 Reuters+

‘Yan majalisar dattawan kasar Kamaru sun bayar da cfa milyan 100 a matsayin gudunwamu ga asusun da gwamnatin kasar ta kafa don yaki da cutar annobar Covid-19.

Talla

Shugaban majalisar kasar Marcel Niat Njfenji, wanda ya bayyana gudunmuwar ya kuma bayyana takaicinsa ga wadanda ke sukar gwamnatin kasar dangane a yadda take tunkarar annobar, yana mai cewa wannan lokaci ne na hadin kai a maimakon nuna son kai irin na ‘yan siyasa.

Bayan da shugaba Paul Biya ya sanar da kafa wata gidauniya domin tara kudaden da za a yi amfani da su don yaki da Coronavirus, shi ma jagoran ‘yan adawa Maurice Kamto ya bude tasa gidauniyar, to sai dai daga bisani gwamnati ta bayar da umurnin rufe asusun kudaden da ya tara, bisa zargin cewa ya saba wa ka’ida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.