Isa ga babban shafi
WHO-Lafiya

Yau ce ranar yaki da malaria, zazzabi mafi kisa a nahiyar Afirka

Malaria, zazzabi mafi kisa a nahiyar Afirka
Malaria, zazzabi mafi kisa a nahiyar Afirka GETTY/DEA PICTURE LIBRARY

Yau ita ce ranar yaki da zazzabin cizon sauro wato malaria, ranar da ke zuwa a daidai lokacin da hankulan duniya suka karkata wajen yaki da cutar Coronavirus.

Talla

A shekarar 2018, sama da mutane milyan 228 ne suka yi fama da wannan zazzabi, inda dubu 405 suka rasa rayukasu, to sai dai hukumar lafiya ta duniya ta ce adadin wadanda za su mutu a bana zai iya kaiwa dubu 700 mafi yawansu a Afirka.

Masana kiwon lafiya sun yi gargadin cewa bai kamata kasashe da kuma kungiyoyi su manta da illolin wannan zazzabi na cizon sauro ba wanda ke haddasa asarar rayukan dubban mutane a kowace shekara.

Yanzu haka akwai fargabar za a iya fuskantar karancin kudi don yaki da wannan zazzabi, lura da yadda karfin duniya ya koma ga batun yaki da Covid-19, alhali an tabbatar da cewa 93% na kananan yara da suka kamu da malaria na rasa rayukansu a nahiyar Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.