Isa ga babban shafi
Najeriya-Coronavirus

A Najeriya, coronavirus ta shiga jihohi 28 gami da Abuja

Wasu magungunan da ake kan gwaji don warkar da covid-19 a duniya
Wasu magungunan da ake kan gwaji don warkar da covid-19 a duniya REUTERS/Dado Ruvic

A Najeriya an tabbatar da samun karin mutane 87 da suka harbu da cutar Covid-19 a jiya asabar, yayin da a karon farko aka samu wanda ya harbu da cutar a jihar Imo da ke kudu maso gabashin kasar.

Talla

Cibiyar Yaki da Cututuka NCDC ta ce, 33 na sabbin mutanen, an same su ne a Lagos, 18 a Borno, 12 Osun, 9 Katsina, a jihohin Kano da Ekiti kuwa mutane hurhudu, yayin da aka samu mutane uku-uku a jihohin Edo da Bauchi sannan mutum daya a jihar Imo.

Wadannan alkaluma na nuni da cewa a Najeriya, an samu mutane 1182 da suka kamu da cutar zuwa yanzu, yayin da adadin wadanda suka rasa rayukansu suka tashi zuwa 35 a jimlice.

Jihohi da kuma adadin mutanen da Covid-19 ta harba a Najeriya zuwa tsakiyar daren asabar 25 ga watan afrilun 2020:

Lagos-689, Abuja-138, Kano-77, Ogun-35, Osun-32, Gombe-30, Katsina-30, Borno-30, Edo-22, Oyo-18, Kwara-11, Akwa Ibom-11,Bauchi-11, Kaduna-10, Ekiti-8, Ondo-4, Delta-6, Rivers-3, Jigawa-2, Enugu-2, Niger-2, Abia-2, Zamfara-2, Sokoto-2 sai kuma jihohin Benue, Anambra, Adamawa, Plateau, da Imo inda aka samu mutum guda-guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.