Isa ga babban shafi

An dage gasar CAF a Kamaru saboda korona

Shugaban CAF Ahmad Ahmad
Shugaban CAF Ahmad Ahmad france24.com

Shugaban hukumar kwallon kafar Afirka, Ahmad Ahmad, yayi karin haske dangane da dage gasar neman cin kofin Afirka da kwamitin zartarwar hukumar ta yi ranar Talata.

Talla

Gasar da aka tsara gudanarwa ranar 9 ga watan Janairun shakara mai kamawa, yanzu an dage zuwa watan Janairun 2022, kuma a Kamaru.

Ahmad Ahmad wanda yayiwa sashin Faransacin Radio Faransa International bayani, yace sun dage gasar ne saboda annobar coronavirus, kuma sai da aka tattauna da mahukuntan kasar Kamaru kuma suka amince kafin aka dage.

Ahmad yace, gasar kwallon kafar Afirka, ba kawai wasan kwallo ba ne, gagarumin buki ne na ‘yan Afirka, don haka baza su so ganin an gudanar da shi, fili wayam ba tare da ‘yan kallo ba.

A bara ne dai Hukumar CAF ta sauya lokacin shirya gasar da ke gudana tsakanin watan Yuni da Yuli, watan Janairu saboda yanayi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.