Isa ga babban shafi

Kasashen Afirka zasu kaddamar da kasuwancin bai daya

Takardar kudin Nairan Najeriya
Takardar kudin Nairan Najeriya PIUS UTOMI EKPEI/AFP

Laraban nan aka shirya kasashen Afirka 54 zasu kaddamar da shirin kasuwancin bai daya a tsakanin su, wanda zai baiwa kasashen damar cinikayya da kuma gudanar da harkokin kasuwanci ba tare da shamaki a tsakanin su ba.

Talla

Sai dai ga alama rashin cimma yarjejeniya da kuma annobar coronavirus ta haifar da tsaiko ga shirin wanda ake saran ya amfani mutane akalla sama da biliyan guda da miliyan 200 da kuma bunkasa tattalin arzikin nahiyar wajen mu’amala a tsakanin su.

Sakatare Janar na kungiyar dake kula da shirin Wamkele Mene yace kowa ya ga matsalolin da suka yiwa shirin tarnaki, inda ayau kasashen Afirka akalla 42 ke killace sakamakon annobar coronavirus.

A baya-bayan nan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana rashin jin dadi da matakin kasashen renon Faransa na janyewa daga shirin samar da kudin bai daya tsakanin kasashen yammacin Afrika, wanda aka yiwa lakabi da ECO, yayinda ya ya gargadi takwarorinsa kasashen da ke cikin tattaunawar kaddamar da kudin kan su tashi tsaye wajen cika sharuddan da aka gindaya domin samun nasarar shirin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.