Isa ga babban shafi
Pakistan-Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya Na Taro don Kai Agaji Pakistan

Mabukata na jiran karban kayan agaji
Mabukata na jiran karban kayan agaji RFI

Kasashen dake cikin Majalisar Dinkin Duniyayau sun fara tattaunawa gameda irin karin agajin da zasu baiwa kasar Pakistan wadda ambaliyar ruwan sama yayi wa ta'adin gaske.Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ne ya kira taron gaggawan na musamman bayan ziyarar daya kai kasar ta Pakistan.Mutane samada miliyan shida n eke dogaro kan abinda zaa basu kuma suna cikin matukar bukatar abinci, ruwa mai tsabta da kuma wurin kwana.Yanzu haka dai akwai fargaban barkewar cutar kwalara da wasu munanan cututtuka a kasar.Taran na yau da akeyi a New York nada niyyar ganin an gaggauta kai kayan agaji ne, kasancewar an sami rabin kayan da ake bukata sun isa kasar. 

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.