Isa ga babban shafi
Pakistan

Ambaliyar ruwa na kara kamari a Pakistan

Wasu daga cikin wadanda Ambaliyar ruwa ya shafa a Pakistan
Wasu daga cikin wadanda Ambaliyar ruwa ya shafa a Pakistan Reuters

Mahukunta da kungiyoyin agaji a Pakistan na fafutikar kare yankin kudancin Singh bayan wani bala’in ambaliyar ruwa da ke neman yin barna a yankin. A jiya lahadi mutane sama da dubu goma da ke zaune a yankin kudancin Sigh musamman mazauna kauyen Shahdadkot tuni suka nemi mafaka bayan da ruwan ya fara barna ga muhallinsu. Ministan kula da ayyukan noman rani Jam Saifullah Dharejo ya bayyana cewa shamakin da aka gina don kariya ga kauyen na Shahdadkot na cigaba da zabtarewa sanadiyar matsalar ambaliyar ruwan. Kodayake ya bayyana cewa suna iya kokarinsu wajen ceton rayukan al’umma.A tsakanin wata daya bala’in ambaliyar ruwan dai ya yi sanadiyar rasa rayukan mutane sama 1,500, al’amarin da kuma ya shafi sama da mutane miliyan 20 kodayake an bayyana rashin samun ambaliyar ruwan a Hyderabad, daya daga cikin manyan biranen na Sigh da ke da yawan Jama’a sama da miliyan biyu.Al'amurra dai a kasar sai ci baya suke yi, al’amarin da kuma ya jefa kasar cikin mawuyacin hali inda al’umma da dama a kasar ke bukatar taimakon abinci hadi da fama da rashin muhalli da karancin magunguna da ya dabaibaye su.A yanzu haka dai hukumar samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana kudirin kai taimako cikin gaggawa na kayan abinci ga miliyoyin mutanen da al’amarin ya shafa.   

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.