Isa ga babban shafi
Iran

Iran ta dakatar da shigo da wasu kayyayakin ketare

Taswirar kasar Iran
Taswirar kasar Iran www.memnav.com/im/IranMap.gif

A kokarin da ta ke yi na ganin cewa ta magance mastalar farin kudaden ketare a kasar, Iran ta dakatar da shigo da kayyayakin more rayuwa kimanin guda 2000 da ake shigo da su daga kasashen. Kasar ta yi hakan ne saboda takunkumin da kasashen Turai suka saka mata.  

Talla

Rahotanni daga kasar na nuna cewa, kayyayakin sun hada kayan shafe-shafe, kwalama, da kayan sawa da kuma kayayyakin alatu har ila yau da motoci da kayan ginagine.

A cewar mataimakin Ministan kasuwancin kasar, Hamid Safdel, yin hakan zai taimakawa kasar wajen rage asarar dalar Amurka biliyan hudu a duk shekara, inda ya kara da cewa kayayyakin da aka hana shigowa da su, akan same su a kasar.

Sai dai ya kara da cewa, kayyayaki irinsu na’ura mai kwakwalwa dad a kayayyakin salula za a iya dawo da shigo da su idan har kasar bazata iya samarwa kanta ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.