Isa ga babban shafi
India

wata kotu a Indiya ta ce, gwaje-gwajen magungunna ba kan ka'ida ba a kasar na jawo matsaloli ga koshin lafiyar jama'a

Getty Images/E+/Savushkin

Kotun kolin kasar India ta ce, gwaje-gwajen sabbin magunguna, ba bisa ka’ida ba, da wasu kamfanonin sarrafa magunguna ke yi, na jawo matsalolin lafiya masu yawan gaske a kasar.Kotun ta kuma umarci ma’aikatar lafiyar kasar ta rinka sa ido, kan duk wani gwajin sabbin magungunan da za a yi a kasar ta Indiya. 

Talla

Kotun ta dauki wannan mataki ne a yau Alhamis, yayin sauraren koke, kan kan mace-mace, da matsalolin lafiyar da irin wadannan gwaje-gwajen ke janyo wa mutanen da aka yi gwajin kansu, da kuma yawancinsu an yi gwajen ne a kansu ba tare da sani ko amincewar su ba.

Mai shari’a R.M. Lodha yace akwai batutuwa da dama, da suka shafi doka da hankali, da ya kamata hukumomi su kiyaye, amma ake biris da su.

Alkalin, ya kara da cewa, ana amfani da ‘yan kasar ta Indiya tamkar kayan gwajin magunguna, inda ya umarci sakataren lafiyar kasar da ya mayar da hankali sosai kan lamarin.

Masu koken, da suka hada da wata kungiyar likitoci da ‘yan wata kungiyar sa kai, sun ce araha, rashin dokoki masu karfi, da rashin aiki da dokoki, na wasu daga cikin dalilan da ke sa ana irin wadannan gwaje gwajen ba bisa ka’ida ba.

Kungiyoyin sun ce, sun gabatar da wani rahoton da ke nuna yadda aka yi amfani da marasa lafiya fiye da 200, don gwada magunguna, ba tare da izinin su ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.