Isa ga babban shafi
Iran

Iran na shirin aikawa da dakarun ruwanta a Kogin Mediterranean

shugaban kasar Iran, Mahmoud Ahmedinejad.
shugaban kasar Iran, Mahmoud Ahmedinejad. (Photo : AFP)

Domin ganin cewa ta bunkasa kasancewarta a kogin Mediterrean, kasar Iran zata aika da wani dan karamin tawagar sojinta na ruwa, kamar yadda daya daga babban sojin ruwan kasar ya bayyana. 

Talla

Wannan aikewa da sojin da kasar ta Iran zata yi, zai zamanto karo na uku da ta taba yin haka tun bayan Juyin Juya halin Islama da aka yi, inda jiragen kasar yakin na ruwa suka tsaya a tashar ruwan kasar Syria.

A cewar daya daga cikin manyan hafsan sojin ruwan kasar, Habibollah Sayari, tawagar sojin ruwan zasu ratsa ta Kogin India, Gulf of Eden Bal al- Mandeb da Red Sea da kuma Suez Canal.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.