Isa ga babban shafi
Syria

An killace makamai masu guban kasar Syria

Tawaggar masu sa ido kan makamai masu guban kasar Syria
Tawaggar masu sa ido kan makamai masu guban kasar Syria REUTERS/Phil Nijhuis/Files

A yau Alhamis, tawaggar masu sa ido na kasashen duniya kan makamai masu guban kasar Syria ta killace dukkan makamai masu guba, da hukumomn birnin Damascuss suka nuna musu. Twaggar tace an adana makaman ta inda ba za a iya amfani da su ba.Mai magana da yawun tawaggar ta masu sa idon ta OPCW Christian Chartier yace, yadda suka adana su, ba wanza zai iya keta shingen da suka yi wa makaman na kasar Syria.A cewar Chartier, an sami ton 1000 na sinadaran da za a iya hada makamai da su, baya ga ton 290 na makamai masu guba.Tawaggar ta kara da cewa makaman da sinadara na nan a wuraren da suke, kuma ba a fara kawar da su ba.Yarjejeniyar da kasashen Amurka da Rasha suka cimma, ta baiwa tawaggar nan da tsakiyar shekara mai zuwa ta 2014, don lalata dukkan makamai masu guban kasar ta Syria, da ma wuraren da ake kera su.Wannan matakin ne kawai zai kawar da amfani da karfin soja kan gwamnatin shugaba Bashar al-Assad.Tuni hukumomin kasar ta Suyrai suka bayar da hadin kai kan wannan aikin. 

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.