Isa ga babban shafi
Syria

Rikicin Syria ya lakume rayukan kananan yara-bincike

Wasu yara 'yan kasar Siriya da ke gudun hijira
Wasu yara 'yan kasar Siriya da ke gudun hijira REUTERS/Muhammad Hamed

Sakamakon wani bincike yace sama da yara kanana 11,000 ne suka mutu a rikicin Syria, cikinsu kuma akwai yara 128 da suka mutu sakamakon hare hare makamai masu guba. Wani kamfanin bincike na Britaniya, da ake kira Think-tank ya gudanar da binciken kuma alkalumman sun ce sama da yara kanana 11,000 ne suka mutu yawancinsu ‘yan kasa da shekaru 17. 

Talla

Rahoton Binciken mai taken gaskiyar adadin yaran da suka mutu a Syria, an yi sharhi ne akan rikicin Syria tun barkewar rikicin a watan Maris din 2011 zuwa watan Agustan bana.

A cikin rahoton an bayyana cewa yara 128 ne suka mutu a watan Agusta kawai sakamakon hare haren makamai masu guba da aka kai a Ghouta, da ke kusa da Damscus, wanda aka dora alhakin kai harin ga shugaba Bashar al Assad.

Kuma binciken yace adadin yara maza da suka mutu sun zarce mata, wadanda tsautsayi ke rutsawa da su a lokacin ake kokarin kai wa masu manyan shekaru hari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.