Isa ga babban shafi
Malaysia

Malaysia: Jirgi MH370 ya yi hadari ne a tekun India

Firaministan kasar Malaysia Najib Razak a lokacin da ya ke bayar da sanarwar faduwar jirgin kasar a teku
Firaministan kasar Malaysia Najib Razak a lokacin da ya ke bayar da sanarwar faduwar jirgin kasar a teku REUTERS/Edgar Su

Firaministan kasar Malaysia Najib Razak ya bayar da sanarwar cewa Jirgin saman kasar da ya bata sama da makwani biyu da suka gabata dauke da fasinjoji 239, ya fadi ne a cikin tekun India, kuma yace dukkan mutanen da ke ciki jirgin sun rasa rayukansu.

Talla

Firaministan yace sun tabbatar da haka ne daga gamsassun bayanai a tauraron dan Adam a yankin da jirgin ya fadi a teku.

Akwai sakon kar-ta-kwata da gwamnatin Malaysia ta aikawa ‘yan uwan mutanen da ke cikin jirgin da ya bata mai dauke da sakon cewa jirgin ya bata kuma babu fasinjan da ya rayu a cikinsa.

Kasashe da dama ne suka shiga aikin neman jirgin Malaysia a tekun India kusa da Australia bayan an hango wasu abubuwa masu kama da tarkacen jirgin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.