Isa ga babban shafi
Malaysia-China

Masu bincike sun hangi wani abu na Jirgin Malaysia MH370 a karkashin Teku

Sojin Ruwan Australia masu binciken jirgin MH370
Sojin Ruwan Australia masu binciken jirgin MH370 REUTERS/Australian Defence Force/Handout via Reuters

An hango wani abu a karkashin Teku kamar Akwatin bayannai ta Jirgin Malaysia. Jami’an Sojin Ruwan kasar Australia ne suka bayyana hango wani abu a karkashin Teku da suka ce ya yi kama da Akwatin adana bayannai ta Jirgi

Talla

Babban jami’in gudanarwa na binciken Jirgin jigilar Fasinjan kasar Malaysia MH370 da ya bata wato Angus Houston ya yi karin bayani, inda yake cewar yankin da suka samu wannan bayannai da suke gabatarwa ga jama’a na da zurfin akalla mitoci 4,500 a karkashin Teku.

Kuma a cewar Angus Houston zurfin Ruwan Tekun ka iya takaita aikin da suke har na tsawon lokaci, yace gaskiya zai fada cewar abin na iya daukar kwanaki kamin su samu cikakkun bayannai, don haka da sauran Rina a Kaba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.