Isa ga babban shafi
Gaza

Ana shigar da kayan agaji zuwa Gaza

Falasdinawa da ke rayuwa a wata Makarantar Majalisar Dinkin suna shirin komawa gida a gabacin Khan Younis da ke kudu da zirin Gaza
Falasdinawa da ke rayuwa a wata Makarantar Majalisar Dinkin suna shirin komawa gida a gabacin Khan Younis da ke kudu da zirin Gaza Reuters

Kasashen duniya na ci gaba da aikewa da kayan agaji zuwa Yankin Gaza don tallafawa Falasdinawan da suka tagayyara sakamakon kwashe kwanaki 50 ana fafatawa tsakanin kungiyar Hamas da Israila abin da ya yi sanadiyar kashe Falasdinawa sama da 2,000.

Talla

Ya zuwa yanzu sama da ton 200 na agaji daga kasashen Saudi Arabia da Oman da Turkiya suka isa Yankin, yayin da hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta aike da abincin da mutane 150,000 zasu ci na kwanaki biyar.

Mayakan Hamas ta yi alkawalin bayar da tallafi domin gina sabuwar Gaza da Isra’ila ta tarwatsa a tsawon makwanni bakwai tana kai farmaki, bayan yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cim ma ta fara aiki a Gaza.

Tun a daren Talata ne Mutanen Gaza suka bazama saman titi suna murna, bayan an shafe tsawon kwanaki 50 ana fafatawa tsakanin Sojojin Isra’ila da Mayakan Hamas.
Shugabannin Hamas dai sun ce wannan nasara ce suka samu akan Isra’ila, amma Firaminista Benjamin Natenyahu ya yi watsi da ikirarin.

Natenyahu yace sun ruguza Kungiyar Hamas kuma ba ta samu biyan bukata koda guda daga cikin sharuddan da ta gabatar ba.

Akalla Falasdinawa 2,140 ne Isra’ila ta kashe yawancinsu fararen hula yayin da kuma Sojojin kasar 64 suka mutu.

Kungiyar Kasashen Turai ta dai yaba da rawar da kasar Masar ta taka wajen kulla yarjejeniyar kawo karshen yakin da shi ne mafi muni a cikin shekaru goma tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas a yankin Gaza.

Sanarwar da kungiyar ta fitar, ta bukaci a ci gaba da tattaunawa domin kulla yarjejeniyar da zata dore domin samun zaman lafiya a Yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.