Isa ga babban shafi
China

Wani Mahaifi a china ya kashe Malamar Diyarsa da Wuka

chinapost.com.tw

Wani mutum a kasar China da aka ki daukar ‘yarsa a wata makarantar furamare, ya kutsa kai a makarantar inda ya kashe wata malama da wasu Dalibai uku da Wuka, ya kuma raunata wasu Dalibai 5

Talla

Maharin da aka bayyana sunan sa a matsayin Chen Yanfu ya kuma hau Benen Makarantar mai hawa 5 ya diro ya kuma mutu nan take.

Yanzu haka dai an ce 5 daga cikin Daliban da Mutumin ya jikkata na kwance a Assibiti, dai daga cikinsu kuma na halin Rai kwakwai mutu kwakwai ne.

Malamar Makarantar dai ya kashe ta ne ta hanyar suka da Wuka a Ciki, ta kuma mutu Saoi kalilan da aukuwar harin.

Shugaban Makarantar ya ce Maharin mai shekaru 43 bai cewa kowa kala bad a shigarsa cikin Aji kawai ya fito da Wuka ya kuma kama sukar kowa ya samu a cikin Aji.

Mutumin dai ya hasala ne akan rashin baiwa ‘yarsa damar shiga Makarantar, kuma yanzu haka ‘yansanda na binciken yadda lamarin ya kasance.

Harin kuma ya auku ne a ranar farko ta bude Makarantu a kasar ta China, sannan alkalumman hukuma sun nuna cewar hakan ta sha faruwa a kasar ta China inda a shekarar 2010 ma an kashe mutane 17 kuma 15 daga cikinsu, kananan Yara ne a yayin da aka jikkata 80.

A Watan Maris da ya gabata ma wani mutum ya kashe wasu ‘yan uwan juna guda biyu , ya kuma karci wasu 11 da Wuka daga cikinsu hadda kananan Yara 6 a wajen wata Makarantar Furamare mai zaman kanta a shanghai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.