Isa ga babban shafi

'Yan rajin tabatar da Democradiyya sun sake zanga zanga a Hong Kong

Mazu zanga zanga a Hong Kong, suna tattaki jiya Lahadi.
Mazu zanga zanga a Hong Kong, suna tattaki jiya Lahadi. REUTERS/Tyrone Siu

Dubban mutane masu goyon bayan Dimokradiyya ne suka gudanar da zanga-zanga a manyan Titunan birnin Hong Kong. Wannan zanga zance ta farko tun bayan da aka gudanar da wata zanga-zangar, da ta dakatar da al’amurra baki daya a birnin har na tsawon Watanni 2 a baya.An hangi dandazon masu zanga-zangar rike da Lema mai kalar ruwan dorawa, suna tafiya a hankali a kan Titunan birnin na Hongkong, a yayin da masu zanga-zangar ke kuwwar neman ‘yancin jefa kuri’a, a Dimokradiyyance.Sai dai ba kamar yanda aka zata ba, yawan masu zanga-zangar bai cika ba, domin kasa da mutane dubu 13 ne kawai suka halarta, kamar yadda masu shirya zanga-zangar suka sanar.Dama dai an yi hasashen samun mutane Dubu 50 ne, amma kuma a ta bakin masu shirya zanga-zangar, al’amarin ya kayatar matuka.Ofishin ‘yan sandan birnin na Hongkong dai ya ce akalla mutane Dubu 8,800 ne suka shiga zanga-zangar, adadin daya sha banban da na masu shirya zanga-zangar.Hukumomin Hongkong dai basu ce komai akai ba, a yayin da al’amurra ke dada zafafa, harma ana ganin da wuya zanga-zangar bata zama matsala ba.A wancan karon dai akalla muatane Dubu 100 ne suka halarci zanga-zangar da kuma ta haddasa tashin hankali, amma sannu a hankali al’amurra suka rinka lafawa. 

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.