Isa ga babban shafi
Japan

Okawa ta yi bikin cika shekaru 117 a Japan

Misao Okawa, Matar da ta fi tsufa a duniya.
Misao Okawa, Matar da ta fi tsufa a duniya. REUTERS

Matar da ta fi tsufa a duniya Misao Okawa, ta yi bikin cika shekaru 117 a yau Alhamis cikin koshin lafiya a yammacin  kasar Japan. Okawa ta yi bikin ne tare da ‘yayanta guda uku da jikokinta. An fi samun ma su manyan shekaru a kasar Japan inda Namijin da ya fi tsufa a duniya ma yana kasar, Sakari Momoi mai shekaru 112.

Talla

Okawa ta karbi faranni da dama daga mutanen da suka taya ta murnar cika shekaru 117 a duniya cikinsu har da babban yaronta Hiroshi mai shekaru 92.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.