Isa ga babban shafi
Indonesia

Adadin mutane 142 suka mutu a hatsarin jirgin Indonesia

Hadarin Jirgin sojin kasar Indonesia.
Hadarin Jirgin sojin kasar Indonesia. REUTERS/Irsan Mulyadi/Antara Foto

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon hatsarin jirgin saman sojin Indonesia jiya Talata da ya abka kan gidajen jama’a ya kai 142, yayin da ake ci gaba da aikin ceto a inda Jirgin ya fadi a yankin Medan.

Talla

Jirgin kirar Hercules C-130 ya fadi ne a garin Medan jim kadan bayan tashinsa a tsibirin Sumatra dauke da jami’an soji da iyalansu.

Rahotanni sun ce gidaje sun rushe, motoci sun kama da wuta yayin da jirgin mai shekaru 51 gaba daya ya lalace.

Ana ganin adadin wadanda suka mutu na iya zarce haka

Sau biyu ke nan ana samun hatsarin jirgi a birnin Medan mai yawan jama’a kimanin Miliyan biyu, inda a 2015 aka samu hasarar rayukan mutane 150 a lokacin da wani Jirgin Mandala ya yi hatsari.

Babban hafsan sojin kasar Agus Supriatna da ya ziyarci wurin da hatsarin ya auku ya ce babu wanda ya tsira daga cikin jirgin.

Shugaban Indonesia Joko Widodo ya bayyana damuwarsa kwarai dangane da hatsarin tare da jajanta wa Iyalan wadanda suka rasa rayukansu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.