Isa ga babban shafi
Malaysia

An ga tarkace da ake tunanin na Jirgin Malaysia ne

Ana tunanin tarkacen da aka tsinta a Tekun India na jirgin Malaysia ne Boeing 777 ko MH370 da ya bata
Ana tunanin tarkacen da aka tsinta a Tekun India na jirgin Malaysia ne Boeing 777 ko MH370 da ya bata REUTERS/Zinfos974/Prisca Bigot

Mahukuntan Malaysia sun ce tarkacen jirgin da masu bincike suka tsinta a tekun Indiya na jirgin kasar ne mai lamba 777, yayin da wasu ke tunanin ko tarkacen jirgin kasar ne mai lamba MH370 da ya bata babu labarinsa.

Talla

A shafinsa na Facebook Firaministan Malaysia ya ce suna kan bincike domin tantance ko tarkacen da aka tsinta Jirgin kasar ne MH370 da ya bata akan hanyarsa daga Kula Lumpur zuwa Beijing a bara.

Wata tawagar kwararri ce ta isa tsibirin Réunion a yankin Tekun Indiya mallakin Faransa a safiyar yau alhamis domin binciken wasu buraguza wani jirgin sama da ake zaton cewa na Malaysia Airlines ne wanda ya bata tun cikin watan Maris na shekarar bara dauke da mutane 239 a cikinsa,

A jiya laraba ne dai aka bayar da labarin cewa an ga wani bangare na jirgin sama mai tsawon mita biyu akan tekun, abin da kuma ake zaton cewa na wancan jirgin mallakin kasar Malaysia ne da ya bata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.