Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falasdinawa

Hamas ta gargadi Isra'ila kan kisan Falasdinawa

(shugaban Hamas Hamas, Khaled Mechaal) Le leader du mouvement palestinien Hamas, Khaled Mechaal, photographié en 2012 à Tunis.
(shugaban Hamas Hamas, Khaled Mechaal) Le leader du mouvement palestinien Hamas, Khaled Mechaal, photographié en 2012 à Tunis. AFP PHOTO / KHALIL

Kungiyar Hamas ta gargadi kasar Isra'ila da ta yi hattara bayan harin jiragen saman da ta kai a yangin Gaza ya hallaka wata Bafalasdina mai juna 2 da karamar 'yar ta har lahira.A dai dai wannan lokaci da rikici tsakanin matasan Falasdinawa da dakarun Isra'ila ke  kamari a yankin gabashin birnin kudus, da ke neman juyewa ya zuwa sabuwar gwagwarmayar neman ‘yanci ta Intifada. 

Talla

A jiya lahadi kasar Isra'ila ta kai harin jiragen saman a yankin na Gaza a matsayin mayar da martani kan harbin makamain Roka daga yankin na Gaza da na’urar kakkabo makamai masu linzami.

Har ila yau Rundunar sojan kasar Isra'ila ta yi nasarar warware wani bam da aka shirya kai harin ta’addaci da shi a birnin Tel Aviv babban birnin kasar.

Makamin Rokar da aka kakkabo dai ya kasance irinsa na 2 da aka harba akan kasar ta Isra'ila daga yankin na Gaza tun ranar Juma’ar da ta gabata kawo yanzu.

Yankin gabashin zirin Gaza dai, da kawo yanzu ke gefe guda, daga shiga rikicin dake ci gaba da zafafa a gabar yammacin kogin Jodan, sannu a hankali ya fara tsintar kansa a rikicin.

Kisan da aka yiwa Bafalasdinuwar mai juna 2 Nur Hassan 'yar shekaru 30 a duniya da karamar 'yar ta, ya sake jefa yarjejenniyar tsagaita bude wutar da ake aiki da ita tun karshen watan Ogustan 2014, tsakanin Isra'ila da yankin na Gaza.

A nasa bangaren kakakin kungiyar Hamas Sami Abou Zouhri, ya ce sun gargadin kasar Yahudun Isra'ila da ta yi hattara kan ayyukan rashin hankali da tunani da ta ke aikatawa a kan Falasdinawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.