Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falasdinawa

Ana zargin Isra'ila da yunkurin sake tayar da boren Intifad

Boren Intifad a shekara ta 1987
Boren Intifad a shekara ta 1987 Menahem Kahana/AFP

Ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin Palasdinawa da Yahudawa a yankin Gabas ta Tsakiya inda ministan harkokin wajen Palasdinawa Riad al Maliki, ya zargi Isra’ila da kokarin tayar da boren intifada a karo na uku.

Talla

Ministan harkokin wajen na Palasdinawa ya sheda wa kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP cewa, Fira minista Benjamen Natanyahu, yana amfani da wannan rikici ne don kare irin matsalolin da yake fuskanta a fannin siyasa da diplomasiya.

Al Maliki ya ce Natanyahu, ya tafka babban kuskure na karya yarjejeniyar da sassan biyu suka ginu akan ta game da yankin da ya kunshi daya daga cikin wurare mafi tsarki na musulmi, wato masallacin Kudus.

Yayin da ya ke kiran Isra’ila da ta gudanar da al’amuranta bisa tanadin dokokin kasa da kasa, ministan na Palasdinawa ya ce har yanzu, akwai hanyar iya warware matsalar.

Sakamakon barkewar sabon rikici tsakanin Palasdinawa da Yahudawa, matasan Palasdinawa dun daba wuka wa ‘yan Isra’ila 18 yayin da kuma Isra’ilar ta kai hari kan yankin Gaza.

A cikin watan jiya ne kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince a daga tutocin Palasdinu da fadar Paparoma ta Vatican a Majalisar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.