Isa ga babban shafi
Isra'ila

Isra'ila za ta killace Falasdinawa a birnin Kudus

Firaminstan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Firaminstan Isra'ila Benjamin Netanyahu REUTERS/Flavio Lo Scalzo

Majalisar tsaron kasar Isra’ila ta bada umurnin killace yankin da Falasdinawa suke zama a cikin birnin Kudus dan dakile tashin hankalin da ake ci gaba da samu dake da nasaba da harin da ake kai wa da wukake.

Talla

Ofishin Firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya ce majlaisar ta dauki matakai da dama da suka hada da killace yankin da kuma murkushe duk wanda aka samu dauke da makami.

Akalla Yahudawa 7 aka kashe a tashe tashen hankulan na baya bayan nan, yayin da jami’an tsaron Isra’ila suka kashe Falasdinawa 30.

Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya, Ban Ki-Moon ya bukaci Isra’ila da ta sake nazari sosai kan yadda Jami’anta ke amfani da karfin da ya wuce kima a fafatawa da Falasdinawa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.