Isa ga babban shafi
china

Guguwa ta kashe mutane 78 a China

Guguwa mai saurin kilomita 125 a sa'a guda ta kashe mutane 78 a China
Guguwa mai saurin kilomita 125 a sa'a guda ta kashe mutane 78 a China Reuters/Babu

Mutane 78 aka tabbatar da mutuwarsu yayin da wasu kusan 500 suka samu raunuka sakamakon wata guguwa mai dauke da ruwan sama da ta mamaye yankin Jiangsu da ke gabashin kasar China.

Talla

Kamfanin dillancin labaran Xinhua ya ce, ruwa ya mamaye wasu kauyuka  yayin da itatuwa suka fadi lokacin da guguwar mai saurin kilomita 125 a kowacce sa’a, ta ratsa kan Yancheng.

Yanzu haka an ruwaito cewar mutane kusan 200 na can dauke da raunuka daban daban.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.