Isa ga babban shafi
INDIA

Mayaka sun kashe sojoji 17 a yankin Kashmir

Sojoji 17 sun mutu a harin da mayaka suka kai a hedkwatar sojoji a yankin Kashmir.
Sojoji 17 sun mutu a harin da mayaka suka kai a hedkwatar sojoji a yankin Kashmir. Reuters

Akalla sojoji 17 ne suka mutu a yankin Kashmir na kasar India sakamakon arangamar da ta auku tsakanin sojojin da mayakan da suka afkawa hedkwatar sojin a safiyar yau lahadi.

Talla

A cewar kwamandan rundunar sojin Yankin, yace sun yi nasarar kashe 4 daga cikin mayakan a yayin musayar wuta kuma sun cigaba da bin sahun sauran mayakan da suka tsere a yayin da sojin suka ci karfinsu.

Al’ummar yankin sun ce sun wayi gari da jin karar bindigogi da hayakin da ya mamaye sarrarin samaniya, da kuma sintirin jirage masu saukar ungulu.

Gwamnatocin kasashen India da Pakistan sun dadde suna kokarin warware rikici a tsakaninsu game da yankin na Kashmir ba tare da samun nasara ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.