Isa ga babban shafi
Afghanistan

Dusar kankara ta hallaka mutane 54 a Afghanistan

Wani dan Afghanistan da ke tafiya tsakanin itatuwa da dusar kankara ta lullube
Wani dan Afghanistan da ke tafiya tsakanin itatuwa da dusar kankara ta lullube

Saukar dusar kankara a kasar Afghanistan yayi sanadiyar mutuwar mutane 54 yanzu haka, yayin da ake fargabar cewar addain na iya tashi.

Talla

Mohammed Omar Mohammed, mai Magana da yawun ma’aikatar kula da hadura, yace bayan wadanda suka mutu, wasu 52 sun samu raunuka daban daban.

Jami’in yace gidaje 168 suka lalace, yayin da shanu 340 suka mutu sakamakon saukar dusar kankarar.

A gefe guda kuma, kakakin 'yan sandan yankin Balkab na lardin Sari Pul,Zabiullah Amani, da ke arewacin kasar ta Afghanistan, ya ce akalla mutane 70 dusar kankarar ta danne ana kuma kan kokarin ceto su, yayinda wasu 5 suka rasa rayukansu.

A halin yanzu Amani ya ce baki dayan hanyoyin da ke zuwa yankin na Balkab a rufe suke sakamakon yawan da zubar dusar kankarar yayi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.