Isa ga babban shafi
Masar

Harin bam ya kashe mutane 44 a Masar

Mujami'ar dake Tanta da aka kai harin farko a Masar.
Mujami'ar dake Tanta da aka kai harin farko a Masar. REUTERS/Mohamed Abd El Ghany

Shugaba Abdel-Fatah al-Sisi ya ayyana dokar ta baci ta watanni uku sakamakon jerin hare-haren ta’addanci da aka kai akan mujami’u da ya yi sanadiyar rayukan mutane arba’in da hudu a yau lahadi.

Talla

An dai kai hare-haren ne akan mujami’un dake a biranen Tanta da Alexandria a safiyar yau lahadi a daidai lokacin da mabiya ke gudanar da ibada.

Tuni dai kungiyar ISIL ta dauki alhakin kai hare-haren biyu.

Rahotanni a kasar na cewa ISIL ta kai farmakin farko kan cocin Mar Girgis da ke birnin Tanta, in da mutane da dama suka mutu.

Sannan an kai hari na biyu kan Mujami’ar Saint Marks da ke Alexandria, in da mabiya ke tsakiyar bikin tunawa da ranar da Yesu Al-Masihu ya samu nasarar kutsawa cikin birnin Kudus.

Hukumomin Masar sun yi alla-wadai da harin wanda suka ce an kitsa shi don kawo rarrabuwar kawuna a kasar.

A daya bangaren shugaban Darikar Katolika a Duniya Paparoma Francis da ke shirin kai ziyara kasar ya meka sakon ta’azziyarsa ga al’ummar kasar Masar kan asarar rayukan da aka samu sakamakon harin na yau da ya hallaka mutane fiye da arba’in.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.