Isa ga babban shafi
Saudiya-Qatar

Saudiya ta umarci Qatar ta kwashe dabbobinta 12,000

Rakuma, mallakin makiyaya 'yan kasar Qatar da ke tsallaka iyakar Saudiya domin komawa Qatar.
Rakuma, mallakin makiyaya 'yan kasar Qatar da ke tsallaka iyakar Saudiya domin komawa Qatar. Reuters

Rakuma da Raguna sama da dubu 12 ne mallakin wasu attajirai da makiyaya ‘yan kasar Qatar, mahukuntan Saudiyya suka bukaci a kwashe daga cikin kasarta domin komawa da su Qatar.

Talla

Matakin dai yana daga cikin jerin takunkuman da kasar Saudiyya da kawayenta ke ci gaba da dauka a kan Qatar bisa zargin goyon bayan ta’addanci.

Rakuman dubu 7 da kuma raguna dubu 5 sun share tsawon shekaru suna kiwo a cikin Saudiyya, kamar yadda jaridar The Peninsula da ake bugawa a Doha ta bayyana.

An dai share tsawon shekaru da attajirai da kuma sauran makiyaya ‘yan kasar ta Qatar suka mallaki filayen da aka killace, domin kiwon rakuma a sassa da dama da ke cikin Saudiyya, wadanda a yanzu aka bukaci su tattara nasu yanasu su bar kasar a cikin hanzari.

A ranar 5 ga wannan wata na Yuni, Saudiyya ta jagoranci wasu kasashen Larabawa da dama domin katse huldar diflomasiyya, kasuwanci da ma zirga-zirgar jiragen sama da kasar ta Qatar bisa zargin cewa tana goyon bayan kungiyoyin ‘yan ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.