Isa ga babban shafi
Saudiya-Qatar

Kasashen Larabawa sun gindayawa Qatar sharudda 13

Daya daga cikin tankokin yakin kasar Turkiya, a sansanin sojin da gwamnatin Turkiya ta kafa a babban birnin kasar ta Qatar, wato Doha.
Daya daga cikin tankokin yakin kasar Turkiya, a sansanin sojin da gwamnatin Turkiya ta kafa a babban birnin kasar ta Qatar, wato Doha. ©Qatar News Agency/Handout via REUTERS

Kasashen Larabawa da suka yanke hulda da kasar Qatar, sun bayyana jerin ka’idoji 13, da suke son kasar ta cika, kafin dage takunkuman da suka kakaba mata, bisa zarginta da goyon bayan ta’addanci.

Talla

Rufe gidan talabijin mallakinta na Ajazeerah, na daga cikin ka’idojin da Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Masar da kuma Bahrain suka ce dole Qatar din ta cika. Zalika kasashen larabawan sun bukaci gwamnatin Qatar ta rufe gidan Talabijin na Arabi21.

Kari daga cikin ka’idojin da kasashen Larabawan suka gindaya wa Qatar, wadanda suka ce tilas ta cika a kwanaki 10, sun hada da yanke hulda da kasar Iran, kungiyar ‘yan uwa musulmi ta masar, kungiyar Hezbolla ta Lebanon, da sauran kungiyoyi da dama, sai kuma rufe sansanin sojin da Turkiya da kafa don horar da sojin ta. Sai kuma biyan wasu makudan kudade da ba’a bayyana yawansu ba a matsayin diyya.

Koda yake kai tsaye gwamnatin Qatar bata maida martani kan wadannan ka’idoji ba, a makon da ya gabata ministan harkokin wajen Qatar, Shiekh Muhd bin AbduRahman al-Thani, yace kasar ba zata fara wata tattaunawar neman sulhu ba har sai kasashen Larabawan karkashin jagorancin saudiyya sun fara janye takunkuman yanke alaka da ita, da suka dauka.

Makwanni biyu kenan aka kwashe tub bayan da kasashen larabawan suka kakabawa Qatar takunkuman da haryanzu bai yi tasiri kanta kamar yadda suka bukata ba, sakamakon tallafin da ta ke samu daga kasashen Turkiya da Iran na abinci da sauran kayayyakin bukata ta hanyar jiragen sama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.