Isa ga babban shafi
Asiya

Ambaliyar ruwa ta hallaka mutum 700 a kudancin Asiya

Ambaliyar ruwan wadda ta fara tun ranar 10 ga watan Agusta a Indiya da Bangaladesh da Nepal ita ce mafi muni a shekarun baya bayan nan.
Ambaliyar ruwan wadda ta fara tun ranar 10 ga watan Agusta a Indiya da Bangaladesh da Nepal ita ce mafi muni a shekarun baya bayan nan. Reuters

HUKUMONIN A Yankin kudancin Asia sun ce akalla mutane 700 aka tabbatar ambaliyar ruwa ta kashe, yayin da sama da miliyan guda suka rasa matsugunan su. Ambaliya mafi muni tun bayan ta shekarar 2008 da ta halaka kimanin mutum 300.

Talla

Akalla mutane 100 suka mutu a dare daya a kasashen India da Bangladesh sakamakon ambaliyar wadda aka fara samun ta a kudancin Asia tun daga ranar 10 ga wannan wata.

Anirudh Kumar, babban jami’in agajin gaggawa a India yace lamarin yafi kamari a Jihar Bihar inda mutane 53 suka mutu.

Kumar yace ya zuwa yanzu mutane 205 suka mutu sakamakon ambaliyar, yayin da kusan 400,000 suka samu mafaka daga mutane miliyan 10 da ambaliyar ta shafa.

Jami’in yace a Jihar Uttar Pradesh mutane 69 suka mutu, sai kuma Yammacin Bengal mai 122.

A kasar Bangladesh ambaliyar ta shafi yankuna 31 daga yankuna 64 dake kasar, kuma hadarin ya hallaka mutane 115, yayin da ambaliyar ta shafi kusan mutane miliyan 6.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.