Isa ga babban shafi
India

An daure shugaban addini da ya yi wa mata fyade a India

Ana zargin Gurmeet Ram Rahim Singh ya yi wa mata Fyade da dama
Ana zargin Gurmeet Ram Rahim Singh ya yi wa mata Fyade da dama PUNIT PARANJPE / AFP

Wata Kotu a India ta daure shugaban wani addini Gurmeet Ram Rahim Singh shekaru 10 a gidan yari bayan samunsa da laifin fyade ga wasu mata mabiyansa guda biyu.

Talla

An yankewa Gumreet Ram Rahim Singh hukuncin ne cikin tsatsauran matakan tsaro sakamakon tashin hankalin da aka samu makon jiya wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 38, lokacin da aka tabbatar da laifi akansa.

Lauyan matan da aka ci zarafinsu, Utsav Singh Bains ya ce akwai wasu irin wadannan korafe-korafen fyade har 48 da suke zaton ko an kashe matan ko kuma tsoro ya hana su magana.

Lauyan ya ce bukatar su ita ce na ganin an daure shugaban addinin rai da rai saboda laifin da ya aikata.

Hukumomin sun baza jami’an tsaro sassan birnin Rohtak inda ake tsare da Singh domin magance duk wata barazana.

Tuni aka tsare manyan jami’an Singh sama da 100 domin kaucewa tashin hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.