Isa ga babban shafi
Syria-Iraqi

Akwai yiwuwar har yanzu al-Baghdadi yana raye - Amurka

Shugaban kungiyar IS Abu Bakr al-Baghdadi, da ake takaddama kan ikirarin kashe shi.
Shugaban kungiyar IS Abu Bakr al-Baghdadi, da ake takaddama kan ikirarin kashe shi. Social Media Website via Reuters

Rundunar sojin Amurka ta ce akwai yiwuwar har yanzu, shugaban mayakan kungiyar IS Abubakar Al-Baghdadi yana raye.

Talla

Sabon rahoton da, Janar Stephen Townsend, wani babban kwamandan sojin Amurka ya bayyana, ya ci karo da ikirarin ma’aikatar tsaron Rasha na cewa, sojinta sun halaka al-Baghdadi a wani farmakin jiragen yaki, da suka kai kan maboyarsa a birnin Raqqa na Syria, a watan Mayu da ya gabata.

A cewar Janar Stephen, suna da kwakkwaran zargin cewa yanzu haka al-Baghdadi yana boye,a daya daga cikin yankunan da ke kan iyakar Iraqi da Syria.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.