Isa ga babban shafi
Falasdinu

Qudus: Sojin Isra'ila sun kashe mutum daya

Zanga-zanga ta balle a kasashen larabawa bayan kalaman Donald Trump.
Zanga-zanga ta balle a kasashen larabawa bayan kalaman Donald Trump. REUTERS / Mohamad Torokman

Ma'aikatar lafiya ta Falsdinu ta ce sojin Isra'ila sun kashe mutum na farko a zanga-zangar da ake yi bayan matakin da Amurka ta dauka na ayyana Qudus a matsayin babban birnin Isra'ila.

Talla

Wanda aka kashe mai suna Mahmoud al-Masri ya gamu da ajalinsa ne a arangamar da aka yi tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zanga a garin Khan Yunis da ke kan iyakar Isra'ila da Gaza.

Sojojin na Isra'ila sun tabbatar da cewa sun harbi mutane biyu a kan iyakar kasar, wadanda suke zargi da kitsa zanga-zangar da ta haifar da tashin hankali.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi fito-na-fito tsakanin Falasdinawa da jami'an tsaron Isra'ila a wurare daban-daban da ke kusa da shingen bakin iyakar Gaza, da gabar yamma, da kuma birnin na Qudus.

Fiye da masu zanga-zanga guda 250 ne ma'aikatar lafiya ta Falsdinu ta ce an raunata a sanadiyyar amfani da harsasan roba da kuma barkono mai sa hawaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.