Isa ga babban shafi
Asiya

An fara wasannin Olympics da kasashe 92

An tanadi kusan nau'ikan wasanni dubu 3 don kawata gasar ta Olympics wadda ke samun halartar kusan kasashen duniya dari ciki har da 8 daga Nahiyar Afrika.
An tanadi kusan nau'ikan wasanni dubu 3 don kawata gasar ta Olympics wadda ke samun halartar kusan kasashen duniya dari ciki har da 8 daga Nahiyar Afrika. REUTERS/Toby Melville TPX IMAGES OF THE DAY

An fara gudanar da wasannin Olympics da Korea ta kudu ke karbar bakoncinta, bayan da aka gudanar da bikin bude filin wasan a safiyar inda akalla kasashe 92 suka fito don nuna tawagarsu ga idon duniya.

Talla

Ana ganin dai wasannin Olympics din a bana za su fi kayatarwa fiye da wadanda suka gabata ganin yadda wannan karon aka tanadi kala-kalar wasanni har guda dubu 3.

Daga nahiyar Afrika kasashen da za su halarci gasar sun hada da Afrika ta kudu da Ghana da Najeriya da Kenya da Madagascar da Marocco da Togo da kuma Eritrea.

Wani abin kayartawa ga bikin bude gasar wasannin Olympics din shi ne yadda kasashen Korea ta kudu da Korea ta arewa suka fito a karkashin tuta guda wato asalin tutar Korea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.