Isa ga babban shafi
Falasdinu

Kasashen Musulmi sun bukaci kafa runduna don kare Falasdinawa

Shugaban Turkiya Tayyip Erdogan tare da wakilan kasashen Musulmi da ke kungiyar (OIC) yayin taron da suka yi a Istanbul babban birnin Turkiya. 18 ga Mayu, 2018.
Shugaban Turkiya Tayyip Erdogan tare da wakilan kasashen Musulmi da ke kungiyar (OIC) yayin taron da suka yi a Istanbul babban birnin Turkiya. 18 ga Mayu, 2018. Arif Hudaverdi Yaman/Pool via Reuters

Shugabannin kasashen Musulmi sun bukaci kafa rundunar hadin gwiwa ta dakarun kasa da kasa, domin baiwa falasdinawa tsaro, bayanda jami’an tsaron Isra’ila suka hallaka akalla falasdinawan 60 a yankin Zirin Gaza cikin wannan makon.

Talla

Shugabannin sun yi kiran ne yayin taron da suka yi a karkashin jagorancin shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan, a Istanbul.

Erdogan wanda ke neman zarcewa a zaben shugabancin kasar da zai gudana a wata mai kamawa, ya kamanta kisan da Isra’ila ke wa Falasdinawan da kisan gillar da sojin Nazi na Jamus suka yi wa Yahudawa yayin yakin duniya na biyu, inda suka hallaka miliyoyi.

Kasashen Musulmin, sun kuma sha alwashin daukar matakan raddi, a fannin Siyasa da tattalin arziki akan duk wata kasa da ta yi koyi da Amurka, wajen maida ofishin jakadancinta zuwa Birnin Kudus daga Tel Aviv, dalilin da ya sa falasdinawa soma sabuwar zanga-zanga a farkon mako mai karewa don adawa da matakin.

Kafin fara zanga-zangar, falasdinawan sun shafe makwanni suna zanga-zanga akan iyakar Isra’ila da Zirin Gaza, domin tilastawa mahukuntan kasar basu damar komawa yankunansu da suka kwace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.