Isa ga babban shafi
Falasdinu

Isra’ila zata gina karin gidaje 1,958 a Zirin Gaza

Wasu daga cikin sabbin gidajen da gwamnatin Isra'ila ta ginawa Yahudawa a shekarar 2017 da suke yankin Nablus a yamma da kogin Jordan.
Wasu daga cikin sabbin gidajen da gwamnatin Isra'ila ta ginawa Yahudawa a shekarar 2017 da suke yankin Nablus a yamma da kogin Jordan. AFP

Wata kungiya mai kula da matsugunnan yahudawa ta ce Isra’ila ta amince da gina karin muhallan yahudawa ‘yan kama-wuri-zauna 1,958 a wani sabon wuri da ke a yankin zirin Gaza.

Talla

Adadin sabbin matsugunnan da hukumomi a kasar Isra’ila suka amince da ginawa, wasu ne daga cikin adadin 2,500 da ministan tsaron kasar ya gabatarwa majalisar zartaswar kasar.

Amincewa da sake gina sabbin gidajen shi ne na farko tun bayan da kasar Amurka ta maida Ofishin jekadancinta zuwa birnin Kudus a ranar 14 ga watan Mayu na wannan shekara, matakin da ya haddasa bore da ya kai ga dakarun Isra’ila suka hallaka Falasdinawa sama da 60 a wuni daya.

Zuwa yanzu akalla Yahudawa 500,000 ne suka zaune a yankunan da Isra’ila ta kwace daga Falasdinawa a yankunan Yamma da kogin Jordan da kuma gabashin Birnin Kudus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.