Isa ga babban shafi
Yemen

Daular Larabawa ta dakatar da hari a Hodeidah

'Yan tawayen da ake dauki ba dadi da su a Hodeidah na Yemen
'Yan tawayen da ake dauki ba dadi da su a Hodeidah na Yemen ®REUTERS/Abduljabbar Zeyad

Gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce, ta dakatar da hare-haren da take goyon-bayan kaddamarwa kan ‘yan tawayen Huthi a tashar jiragen ruwa ta birnin Hodeida da ke Yemen don bai wa Majalisar Dinkin Duniyar damar jagorantar cimma yarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan tawayen.

Talla

A wasu jerin sakwanni ta kafar sadarwar Twitter, Ministan Harkokin Wajen Hadadiiyar Daular Larabawa, Anwar Gargash ya ce, an dauki matakin dakatar da hare-haren ne da zimmar share fagen cimma yarjejeniyar ficewar ‘yan tawayen Huthi daga tashar jiragen ruwan, sai dai ya yi gargadin cewa, akwai yiwuwar ci gaba da gudanar da ayyukan soji a wannan yanki.

Gargash ya ce, sun dakatar da farmakin don bai wa Jakadan Majalisar Dinkin Duniya, Martin Griffith cikakken lokacin lalubo hanyar cimma matsayar, kuma ya yi masa fatan samun nasara.

A cewar Gargash, tun a ranar 23 ga watan Juni, dakatarwar ta fara aiki, yayin da dakarun gwamnati ke dakon sakamakon ziyarar da jakadan na Majalisar Dinkin Duniya zai kai birnin Sanaa da ke karkashin ikon ‘yan tawayen.

A ranar Larabar da ta gabata ne, Griffith ya gana da shugaba Abedrabbo Masur Hadi a kudancin birnin Aden, yayin da bayanai ke cewa, jakadan na ci gaba da kokarin ganin ‘yan tawayen sun mika ikon Hodeidah ga Majalisar Dinkin Duniya.

Makwannin da aka shafe na kai hare-hare a birnin, sun haifar da fargaba game da tsanantan halin da al’umma ke ciki a kasar ta Yemen wadda ta tuni ta girgiza sakamakon shekarun da aka dauka na yake-yake tsakanin ‘yan Huthi da ke samun goyon Iran da kuma gwamnatin kasar, da ke samun goyon bayan kasashen yankin Larabawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.