Isa ga babban shafi

Ana zargin jami’an Saudiyya 15 da hannu a kisan Khashoggi

Jamal Khashoggi dan jaridar Saudiyya da ya bata a Turkiyya.
Jamal Khashoggi dan jaridar Saudiyya da ya bata a Turkiyya. MOHAMMED AL-SHAIKH / AFP

Wani bincike da Jaridar New York Times dake Amurka ta gudanar ya bayyana cewar daya daga cikin mutanen da ake zargi da hannu wajen bacewar dan jaridar Saudi Arabia, Jamal Khashoggi, na hannun daman Yarima Muhammad bin Salman ne.

Talla

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo ke kai gwaro, yana kaiwa mari tsakanin Saudiya da Turkiya kan bacewar dan jaridar.

Rahotan da Jaridar New York Times ta wallafa yace daga cikin wadanda ake zargi da bacewar Kamal Kashoggi akwai jami’an tsaron Yarima Muhammad bin Salman guda 3 da kuma likita guda.

Wannan labari zai dada jefa shakku kan matsayin shugaba Donald Trump wanda ake zargi da kokarin nesanta hukumomin Saudiyyar da bacewar dan jaridar ko kuma hallaka shi.

Majiyar gwamnatin Turkiya tace akalla jami’an gwamnatin Saudiyya 15 ake zargi da kashe Khashoggi a cikin ofishin Jakadancin kasar, yayin da hukumomin Saudiya ke cewa dan jaridar ya fice daga ofishin.

Yunkurin gudanar da bincike gidan Jakadan Saudiya dake Santanbul yaci tura, saboda rashin amincewar hukumomin Saudiyya, yayin da rahotanni suka ce tuni Jakadan ya bar Turkiya zuwa gida jiya da rana.

Yau ake saran Mike Pompeo zai gana da hukumomin Turkiya kan lamarin, yayin kasashen duniya ke cigaba da matsin lamba wajen ganin an bankado abinda ya faru da Kamal Khashoggi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.