Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falasdinawa

An cimma tsagaita wuta tsakanin Falestinawa da Isara'ila

wata fashewa a karkashin hare haren da dakarun Isarela suka kai kan Hamas Hamas a Gaza   12, Nobemba 2018.
wata fashewa a karkashin hare haren da dakarun Isarela suka kai kan Hamas Hamas a Gaza 12, Nobemba 2018. 路透社。

Kungiyoyin gwagwarmayar Falestinawa da suka hada da kungiyar Hamas dake mulkin yankin Gaza, sun bayyana cimma tsagaita wuta kai tsaye da Israela a karkashin jagorancin kasar Masar, tare da bayyana cewa, za su zura ido su ga ko Israelar za ta mutunta alkawalin.

Talla

Shiga tsakanin da Masar ta yi ne, ya bada damar cimma tsagaita wutar tsakanin kungiyoyin gwagwarmayar neman yancin Falestinawan da gwamnatin Sahayuniya.

Sai dai kawo yanzu babau wani karin haske da aka samu daga kasar Israela dake ci gaba da rike bakinta daga barin tsokaci a kan tsagaita wutar ta jiya.

Yankunan Zirin gaza da wanda Isarela ta mamaye sun fada cikin munanan tashe tashen hankulla ne, tun ranar lahadin da ta gabata, tsakanin Sojan Isarela da kungiyoyin gwagwarmayar falestinawa dake dauke da makamai, tashin hankalin da ya zama irinsa mafi muni tun bayan na yakin shekara ta 2014. Da suka gwabza a tsakaninsu.

Kungiyoyin gwagwarmayar Falestinawan sun haraba daruruwan rokoki a kan kasar ta Isarela, a yayinda anata bagaren rundunar sojin Israelar, ta mayar da martani wajen kai hare hare kan sansanonin kungiyoyin gwagwarmayar ta Hamas da Jihad islamique.

Sashen gwagwarmaya da makamai na kungiyar Hamas ya bayyana cewa, ya maidamartani ne sakamakon kutsen da rundunar sojan mamayen Isara’ila ta yi wa yankin na su a ranar lahadin da ta gabata da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 7 mambobi dakarun nuna turjiyar Falestinawa da kuma wani sojan Isarela guda

A cikin wata sanarwar da ya fitar shugaban Hamas Ismail Haniyeh ya bayyana cewa, ’’Dakarun Hamas sun kare kansu da kuma al’ummarsu, daga hare haren rashin da Isareal ke kai masu’’ kuma zasu ci gaba da yin haka nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.