Isa ga babban shafi
Syria

Syria ta dakile farmakin Isra'ila kan rumbun ajiyar makamanta

Daya daga cikin makaman rundunar sojin Syria da suka dakile farmakin da jiragen yakin Isra'ila suka kai kan rumbunan ajiyar makamansu.
Daya daga cikin makaman rundunar sojin Syria da suka dakile farmakin da jiragen yakin Isra'ila suka kai kan rumbunan ajiyar makamansu. Reuters

Kafafen yada labaran Syria sun rawaito cewa, rundunar sojin kasar, ta yi nasarar kakkabo makamai masu linzami da jiragen Isra’ila suka harba a gaf da birnin Damaskas.

Talla

Rahotanni sun ce jiragen yakin na Isra’ila, sun kai farmakin ne kan manyan rumbunan ajiyar makaman sojojin Syria, lamarin da yayi sanadin jikkatar dakarun kasar guda uku.

Sai dai sojin na Syria sun ce, sun yi nasarar kakkabo mafi akasarin makamai masu linzamin da jiragen yakin na Isra’ila suka harba, kafin su isa kan ilahirin rumbunan ajiyar makaman kasar.

A baya dai Isra’ila ta sha kai farmaki kan sassan Syria, kan abinda ta kira cibiyoyin sojin kasar Iran ko rumbunan ajiyar makamanta, wadanda mafi akasarinsu ke kudancin babban birnin Syrian, Damaskas, sai dai farmakin na ranar Talata shi ne na farko da Isra’ila ta kai cikin kasar, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya sha alwashin janye dakarunsa guda dubu 2 da ke kasar.

Sa’o’i kalilan bayan sanar da matakin janye dakarun na Amurka da shugaba Trump yayi, Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce kasarsa za ta ci gaba da kokarin ta dakile duk wani yunkurin kasar Iran wajen fadada karfin sojinta da kuma tasiri kan sauran al’amura a Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.